SIYASAR NIJAR: An Bukaci Yansanda Su Ba Mahaman Ousman Kariya

Mahamman Ousman

Wadansu kungiyoyin rajin demokradiya a jamhuriyar Nijer sun shawarci hukumomin kasar su dauki matakin kare lafiyar dan takarar jam’iyar adawa ta RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman.

Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne bayan da wasu matasa suka tare a kofar gidansa da nufin matsa masa lamba ya yi watsi da kayen da ya sha a zaben 21 ga watan fabrairu

A sanarwar da suka fitar kungiyoyin na gamayyar CCDR sun fara ne da taya Bazoum Mohamed murnar nasarar da ya samu a zaben da ya gabata kamar yadda kotun tsarin mulkin kasa ta tabbatar da shi a matsayin sabon zababben shugaban kasar Nijer da kashi 55.66 daga cikin 100 na yawan kuri’u kafin su gargadi ‘yan siyasa da magoya bayansu, su bada kai bori ya hau.

Hotunan zanga zangar da aka gudanar a birnin Yamai na Nijar, bayan hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

A washegarin fitar da sakamakon da ya tabbatar da nasarar dan takarar na jam’iyar PNDS Tarayya, wasu matasa sun tare kofar gidan abokin karawarsa Mahaman Ousman cikin yanayin fushi suna kiraye kirayen ganin ya kalubalancin kotun tsarin mulkin kasa abinda gamayyar CCDR a ta bakin kakakinta Siraji Issaka ke ganin alama ce ta nuna rashin da’a ga na gaba. Mafari ke nan da ya sa suka bukaci mahukunta su dauki matakn kare lafiyarsa da ta iyalansa.

Kungiyoyin CCDR sun nuna juyayi a game da rasuwar fararen hular nan 137 da ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla a ranar lahadin da ta gabata a gundumar Tilia sannan su ka yi kiran ga Bazoum Mohamed ya dauki matakin hada kan ‘yan kasa bayan rantsar da shi a ranar 2 ga watan Afrilun, suna masu cewa, ya zama wajibi a gare shi ya dama da kowanne dan Nijer a matsayinsa na shugaban dukan ‘yan kasa.

kotun-tsarin-mulkin-nijar-ta-tabbatar-da-nasarar-bazoum

a-na-zargin-magudi-a-zaben-shugaban-kasar-nijar

yan-adawa-a-jamhuriyar-nijar-sun-zargi-hukumomi-da-tsangwamar-su

Saurari cikkaken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci Yansanda Su Ba Mahaman Ousman Kariya-2:00"