Sojojin Najeriya Sun Ce Suna Bayan Gwamnatin Najeriya Daram Dam

Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Kwana kwanan nan hafsan sojin Najeriya ya ja kunnuwan sojojin kasar yana cewa wasusnsu 'yan siyas na zawarcinsu da wata manufa daban haka ma gwamnatin Birtaniya ta fito tace ba zata amince da juyin mulki ba da ba'a yi ta hanyar zaben halar ba

A wani taro da manema labarai daraktan labarai na sojojin Najeriya Manjo Janar John Eneche yace rundunar sojojin na muba'aya ga shugabancin kasar kuma tana bayan wannan gwamnati daram dam.

Injjishi zasu cigaba da yiwa tsarin mulkin kasar biyayya ba tare da yin wata wata ba. Yace duk wani fargaban juyin mulki a kawar dashi domin ba manufarsu ba ce.Yace sojojin Najeriya masu biyayya ne ga tsarin dimukradiya.

Akan zawarcin da aka ce 'yan siyasa na yiwa wasu sojoji Manjo Janar Eneche yace suna daukan matakai. Yanzu suna bukatar lokaci domin gudanar da bincike.

Shi ma kakakin sojojin Birgediya Janar Kukasheka yace sojojin Najeriya gaba daya sun ta'allaka ne kan biyayya ga shugaba Muhammad Buhari da kuma tsarin mulkin kasa. Yace duk yadda za'a yi, zasu yi iyakacin kokarinsu su kare gwamnatin da tsarin mulkin kasar.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Ce Suna Bayan Gwamnatin Najeriya Daram Dam - 2' 47"