SOKOTO: Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 25

Gawarwakin wasu da 'yan bindiga suka kashe

Ya yin da sojojin Najeriya ke ci gaba da farautar ‘yan bindiga a jihar Zamafara, yanzu haka jihar Sokoto dake makwabtaka da Zamfara na ci gaba da fuskantar ‘karin hare-haren ‘yan bindiga..

Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Rakonni da Tsagi da Kalhu da kuma Gi’ire, duk a cikin gundumar Gandi da ke karamar hukumar mulki ta Rabah, inda ‘yan bindigar da ba’a tantance adadinsu ba, suka kai harin bai daya a daren ranar Asabar, suka kuma kashe a kalla mutane 25.

Haka ma a makwanni ukku da suka gabata wasu yan bindiga suka sunkai irin wannan harin a kananan hukumomin Mulkin Isa da Gudu, yayin da ake hasashen yaduwar hare-haren ‘yan bindiga a makwabtan jihar, a dai-dai lokacin da jami’an soji suke ci gaba da fatattakar su daga jihar Zamfara.

Wannan harin na baya-bayan nan na zuwa ne ‘yan makwanni bayan da gwamnan jihar Sokoton Aminu Waziri Tambuwal, ya gudanar da wani taro da dukkan shugabannin hukumomin tsaro dake jihar ta Sokoto, ciki kuwa har da babban kwamandan shiyya ta 8 ta rundunar sojin Nijeriya da ke Sokoton.

Yanzu haka ana zaman dar-dar a garuruwa da dama a yankin gabashin jihar Sokoto saboda fargabar cewa za’a iya kai hari a kowane lokaci, yayin da wasu al’ummomi da dama suka fice daga garuruwansu.

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO: Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 25