Sokoto Zata Zamo Cibiyar Hada -Hadar Noman Rani a Najeriya-Tambuwal

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

Akwai yuwuwar jihar Sakkwato a Najeriya nan gaba kadan zata zamo cibiyar hada-hadar ayukkan noman rani biyo bayan kokarin gwamnatin jihar na duba yuwuwar samarda madatsun ruwa a kananan hukumomi uku.

Yanzu haka kimanin wata daya kenan da ambaliyar ruwa a Jihar Sakkwato ke barazana ga kauyuka da birane da yayi sanadiyyar barnata kayan amfanin gona na miliyoyin nairori tare da ruguza gidaje, da kuma salwantar rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ruguza tituna da gadoji ciki har da gadar Salame wanda yanzu haka ya yanke

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya sanar da haka lokacin da ya ziyarci kananan hukumomin Kebbe da Silame domin jajantawa jama'a akan barnar da ambaliyar ruwa tayi.

Ya jaddada kokarin gwamnati na samar da madatsun ruwa a Raba, Kebbi da kuma Silame domin rage ambaliyar ruwa da kuma bunkasa ayyukan noma.

Tambuwar yayi kira ga gwamnatin tarayya da a gaggauta gyarawa da yashe madatsar ruwa ta Bakolori da Goronyo, domin rashin yin hakan shi ya sa ake samun ambaliyar ruwa a wannan yankin.

Saurari cikakken rahotan Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO ZATA INGANTA HARKAR NOMAN RANI