Sudan ta Kudu na zargin kasar Sudan da kaiwa rijiyoyin manta harin bom

Matattarar mai a Sudan

Jami’ai a kudancin Sudan suna zargin makwabciyarsu kasar Sudan da kai harin bomai a rijiyoyinta na mai

Jami’ai a kudancin Sudan suna zargin makwabciyarsu kasar Sudan da kai harin bomai a rijiyoyinta na mai, wata alama ta baya bayan nan dake nuni da cewa dangantaka tana kara tsami tsakanin kasashen.

Jami’ai da dama, da suka hada da kakakin gwamnati Barnaba Marial Benjamin ya bayyana cewa, jiragen yaki sun jefa boma bomai jiya Laraba a yankin jihar Unity, dake tazarar kilomita 75 daga kan iyakar da kasashen biyu suke takaddama a kai.

Jami’an sun ce harin bom din ya lalata rijiyoyin mai biyu.

Wani kakakin rundunar sojin kasar Sudan Sawarmi Khaled Saad ya yi watsi da zargi da cewa babu kanshin gaskiya a ciki.

Bisa ga cewar Marial, harin ya sabawa yarjejeniyar hana kai hare hare da aka cimma tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu da aka rattabawa hannu a Habasha watan jiya.