Kalaman El-Rufa'i Yunkuri Ne Na Bata Sunan Najeriya - Sule Lamido

Tsohon ministan harkokin waje na Najeriya Alhaji Sule Lamido, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Kuma, ya ce a tsari na Diplomasiyyar kasa da kasa, kalaman gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i yunkuri ne na bata sunan Najeriya a idon duniya.

Alhaji Sule Lamido ya yi wannan bayanin ne a wata hira da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari, biyo bayan kalaman da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i yayi na cewa duk wasu wakilai ko kungiyoyin kasashen waje da za su so yin katsalanda a harkokin zaben da za yi ranar 16 ga watan Fabarairu, “za a maida gawarwakin su kasashen su.”

Tsohon ministan ya ce, gwamnan na magana ne kawai don a san da zaman shi, kuma don yana amfani da girman mukamin sa, amma baya da hurumin yin wadannan kalaman a matsayin sa na gwamna kuma hakan na muzanta Najeriya ne kawai a idon duniya.

Alhaji Sule Lamido ya kuma ce, lafazin da gwamnan yayi ba zai yi wani tasiri ba a zaben da za a yi ta fuskar diflomasiyya. Ya kuma kara tunatar da jama’a akan yadda wasu wakilan kasashen waje suka yi ta kai-da-komo don tabbatar da an yi zaben gaskiya da adalci a shekarar 2015, kuma gwamna El-Rufa'i a wancan karon ya yaba da kokarin kasashen.

A siyasance kuma tsohon ministan ya ce wannan “kada bula ce kawai yake yi.”

Domin karin bayani saurari cikakkiyar hirar Sule Lamdio da Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Kalaman El-Rufa'i Yunkuri Ne Na Bata Sunan Najeriya - Sule Lamido - 3'37"