Syria Da Rasha Sun Musanta Zargin Hanu a Harin Makami Mai Guba

Shugaba Assad na Syria (Hagu) da Shugaba Putin na Rasha (Dama)

Harin makami mai guba ya halaka mutane da dama a Syria, a cewar kungiyoyin dake sa ido da wadanda ke gudanar da ayyukan jin kai a kasar.

Harin wanda ake zargin dakarun gwamnatin Syria ko kuma jiragen yakin Rasha da aikata wa ya faru ne a arewacin yankin kasar dake karkashin ikon ‘yan tawaye.

A cewar masu fafutukar adawa, wannan hari shi ne mafi muni a shekaru shida da aka kwashe ana yakin basasa a kasar.

Jam’iyar adawa ta Syrian National Coalition ta kwatanta lamarin a matsayin “mummunan kisan kare dangi.”

Ita dai kasar ta Rasha ta kore zarge da ake mata na hanu a harin yayin da ita ma gwamnatin Syria ta musanta zargin yin amfani da makami mai guba.

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a gobe Laraba domin tattauna wa kan harin.