Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawan Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya

Takkadama da ta kunno kai ta yunkurin dakushe hurumin mukadashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ja rarrabuwar kawuna a Majalisar Dattawa.

A wani zama da majalisar ta yi da hakkan ya fito fili karara Sanata Ahmad Sani Yerima, ya ce miko sunan da Farfesa Yemi Osinbajo yayi ya kara tabbatar da cewa lallai majalisar tana da cikakken iko kenen.

Wannan alamari ya harzuka Sanata Abaribe, da ya nemi ya nuna cewa shugaban majalisar dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki, tamkar shine ma ya kamaci ya tafiyar da harkokin kasar kasancewa Farfesa Osibajo, ya tafi Addis Ababa, wajan taron shugabanin kasashen Afirka.

Yunkurin Sanata Abaribe, yasa Sanata Kabiru Garba Marafan Gusau, ya soki wannan matsayar inda yake ganin hakan ya zama cin fuska, ya kawo batun da oda ta hamsin da uku kashi na hudu (53/4) wanda ke cewa Sanata bashi da dama idan yana Magana ya bullo da wani abinda bai shafi zance da ake yi ba a wannan lokacin.

Ya kuma umarci Sanata Abaribe, da ya janye wannan furuci nasa domin tsarin mulki ya yi tana jin yadda shugabanci kasa zai kasance idan babu shugaban kasa akwai matakan da tsarin mulki ya shinfida kuma ya zama wajibi a bisu.

Your browser doesn’t support HTML5

Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawan Najeriya - 3'57"