Ana Neman Gudamawa Ga Wadanda Rikicin Boko Haram Ya Raba Da Muhallan su a Yankin Diffa

Wata mota data yi mugun lodi tana ratsawa ta wani sanin 'Yan gudun hijira na Assaga dake yankin Diffa na Nijar.

Wata kungiyar farar hula mai zaman kanta da ake kira CDEV ce ta shirya neman gudumawar.

Mazauna kauyen N' Galewa a yankin Diffa a jamhuriyar Nijar, suna cikin mawuyacin hali, saboda ala tilas suka bar muhallansu cikin watan Yulin bara, bayan da mayakan da ake zargi 'yan Boko Haram ne suka sace musu 'yan uwansu maza da mata da yara su 39, kuma har yanzu babu labarin su.

Wannan ya sa suka bar muhallansu, suka fada mawuyacin hali. Domin haka ne ma wata kungiyar Fara hula da ake kira CDEV, karkashin jagorancin Hajiya Maimuna, ta shirya neman gudumawa daga jama'a da kungiyoyi, domin tallafawa mutanen.

A hirar da suka yi da wakilin Sashen Hausa Sule Mummuni Barma, Hajiya Mainmuna ta shaida masa, a shekarun baya ma, kungiyar ta shirya irin wannan neman tallafai ga wadansu da suka tagayyara, har mutane dubu 40 suka amfana karkashin shirin.

Ga hirar ta su.

Your browser doesn’t support HTML5

Gangamin neman tallafi ga mutane da Boko Haram ta raba da muhallansu