Tana Kasa Tana Dabo a PDP Reshen Jihar Sokoto

Tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa

Yayin da jam'iyyar PDP ke farfadowa a jihar Sokoto bayan ficewar gwamna Wamako da shigowar Bafarawa, sai ga wata dambarwar siyasa ta kunno kai.
Ficewar gwamna Wamako daga jam'iyyar PDP da shigowar tsohon gwamnan jihar Bafarawa cikin jam'iyyar lamuran jam'iyyar sun dauki wani sabon salo lamarin dake son kawo mata wata sarkakiya.

Wata dambarwa na kokarin kunno kai a daidai lokacin da jam'iyyar ke kokakrin yin zaben shugabanninta na jihar Sokoto. Sarki ne ke kokarin shiga tsakanin 'yan jama'iyyar inda wani bangaren ke zargin Bafarawa da yin babakere.

Alhaji Ibrahim Magaji Gusau na daga cikin masu neman takarar shugabancin jam'iyyar. Yace takardar neman tsayawa takara ya je ya bayar aka ce ba zai shiga ofishin jam'iyyar ba sai da izinin Bafarawa. Yace 'yan banga sun saresu sun kuma sassari motocinsu.

Tun farko raba jam'iyyar biyu tsakanin Bafarawa da 'yan jam'iyyar na ainihi shi ya jawo matsala. Yace idan suka fadi zabe a jihar Sokoto to a zargi Bafarawa.

To saidai Bafarawa yace rashin adalci ne a keyi masa. Yace shi a ganinsa uba yake sabili da haka kowa nashi ne. Yace shi bashi da dan takara duk wanda jama'a ke so nashi ne.

Ga rahoton Murtala Faruk.

Your browser doesn’t support HTML5

Tana Kasa Tana Dabo a PDP Reshen Jihar Sokoto - 2'49"