Rigar Kariya Ta Ba Dinkin Tela Ba Ce In Ji Tandja

Magoya bayan Tandja sun yi dafifi su na masa maraba da komawa gida bayan da aka sako shi daga kurkuku ran Talata 10 Mayu, 2011.

Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar, Tandja Mamadou, yace rigarsa ta kariya ba dinkin tela ba ne, Allah ne Ya yi masa, don haka babu mai iya tube masa ita.

Wannan shi ne karon farko da tsohon shugaban yake bayani a bainar jama'a sa'o'i kadan a bayan da wata kotun koli a Yamai ta ce ta cire masa rigar kariya domin ya gurfana gaban kuliya ya amsa tambayoyi dangane da binciken kudaden da yace ya bari a Baitulmalin kasar kafin sojoji su yi masa juyin mulki.

Tandja ya fadawa kafofin yada labaran gwamnati jim kadan a bayan wata ziyara ta ba-sabam ba da ya kai ma shugaba Issoufou Mahamadou a fadarsa cewa rigar tasa tana nan daram.

Wannan batu na rigar kariyar ya taso a ganawar da yayi da shugaba Mahamadou Issoufou, a wannan ziyara da shi Tandja yace ya kan kai irinta domin girmama shugaban kasa a duk lokacin da yayi niyyar zuwa wata kasar waje domin a duba lafiyarsa.

Masana da dama ma sun furta albarkacin bakinsu kan wannan batu na cire rigar kariyar shugaban.

Your browser doesn’t support HTML5

Mamadou Tandja Yace Rigar Kariyarsa Tana Nan Daram - 2'23"