Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Taron Gaggawa Kan Ebola A Afirka Ta Yamma


Ma'aikatan lafiya na kungiyar MSF su na gyara wurin da za a kebe masu fama da Ebola a kasar Guinea.
Ma'aikatan lafiya na kungiyar MSF su na gyara wurin da za a kebe masu fama da Ebola a kasar Guinea.

Barkewar mummunar annobar cutar Ebola a Afirka ta Yamma ta sanya ministocin kiwon lafiya na yankin sun fara taron gaggawa da nufin shata yadda zasu takali wannan batun.

Hukumar kiwon Lafiya ta Duniya, wadda ke daukar nauyin wannan taron kolin kwanaki biyu a Accra, babban birnin Ghana, ta ce cutar Ebola ta kashe mutane 467 a kasashen Liberiya, Guinea da kuma Sierra Leone.

Wannan sabon adadin da aka bayar jiya talata, ya nuna karuwar kashi 38 cikin 100 na wadanda cutar ta kashe daga adadin da aka bayar a makon da ya shige.

Kasashen Afirka su 11 ne suka tura wakilansu zuwa wurin taron, ciki har da na Najeriya.

Baba Yakubu Makeri ya aiko mana da ciakken rahoto.

Taron Gaggawa Kan Cutar Ebola A Afirka Ta Yamma - 3'06"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG