Taraba: Direbobi na shan kwayoyin samun kuzari

A jihar Taraba direbobi da masu sana'ar acaba kwayoyi suke sha kafin su fara aikinsu lamarin da kan haddasa hadura daa rasa rayuka

Yanzu masu shan kwayar suna anfani ne da itatuwan gargajiya da wasu jiko da kwayoyi.

Direbobi da masu hawan acaba suna shan wadan nan abubuwa ne wai domin su samu kuzarin yin ayyukansu. Masu shan kawayoyin sukan taru a tashoshin mota ne ko wurin da masu ababen hawa na haya suke taruwa.

Wasu sun shaida cewa jikon na yi masu anfani. Suna sha ne domin samun karfin aiki domin kada su ji gajiya ko kasala ajikinsu.

A cikin korarsu suna hada abubua da dama da sunan samun karfi. Wasu sun ce idan basu sha ba ba zasu ji dadin jikinsu ba.

Wani Malam Babab Mamman ya bayyana illar shan maganin gargajiya ba bisa kaida ba.Yace idan mutum ya sha magani na wata cuta daban yana iya jawo mashi wata cutar.

Likitan zamani ma yace shan magani ba tare da wani rashin lafiya ba yana da illa. Idan mutum ya sha magani kuma babu cutar a jikin mutum dole ne maganin ya yaki jikin.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: Direbobi na shan kwayoyin samun kuzari - 4' 17"