Taraba: Rikicin 'Yan Takarar Gwamna a Jam'iyyar APC

Shugaba Buhari A taron Shugabannin Jam’iyyar APC Inda Ya Bayyana Niyyarsa Na Sake Neman Wa'adin Shugabanci

Wasu 'yan takara a jam'iyyar APC a jihar Taraba sun mika kukansu gaban kwamitin sasantawa da uwar jam’iyar ta kafa, don sasanta 'yan takara a jihar, karkashin jagorancin gwamnan jihar Nasarawa Tanko Al-Makurra.

Wasu daga cikin 'yan takarar gwamna karkashin jam’iyar APC a jihar Taraba, sun musanta batun cewa an sasanta tsakaninsu, kuma sun yi mubaya'a ga dan takarar da ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyar, Sani Abubakar Danladi.

Shugaban jam’iyar jihar Taraba, Farfesa Sani Yahya, wanda na daya daga cikin 'yan takara takwas da suka kai kukansu ga uwar jam’iyar APC, ya ce sun yi mamaki da wasu ke yada cewa sun janye a fafutukar da suke yi kan batun takarar.

Sai dai kuma wannan na zuwa ne yayin da tuni jam’iyar ta fara gangami yakin neman zabe.

A wata hira da ya yi Muryar Amurka, tsohon mukaddashin gwamnan jihar, Sani Abubakar Danladi, wanda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar ta APC a Taraba, ya yi kira ga sauran 'yan takara da su zo a hada kai domin a ceci jihar.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: Rikicin 'Yan takarar Gwamna a Jihar Taraba - 3'31"