Taraba: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Mutum Da Ya Kashe Karamin Yaro Don Magani

Abubakar Abdulkadir Mutumin Da Ya Kashe 'Dan 'Kaninsa

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Taraba ta kama wani mutum daya kashe wani yaro karami ya kuma sara shi gunduwa –gunduwa.

Shi dai mutumin da aka kama mai suna Abubakar Abdulkadir, mai kimanin shekaru 50 da haihuwa da aka fi sani da Sambo, mazaunin kauyen Alin Gora ne dake cikin karamar hukumar Ardo Kola, dubunsa ta cika ne bayan da ya kashe wani ‘dan kaninsa mai kimanin shekaru hudu da haihuwa, ya daddatsa shi gunduwa-gunduwa kafin daga bisani ya dafa wani sassan jikin yaron.

Mr Yakubu Yunana Babas, dake zama kwamishinan yan sandan jihar Taraba, ya tabbatar da kama wannan mutum, ya kuma ce zasu ci gaba da binciken wannan dan taliki.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Taraba Mr Yakubu Yunana Babas.

To sai dai kuma da yake amsa tambayoyin manema labarai, Abubakar Abdulkadir, ya ce ya dafa naman yaron nema domin yin magani.

Haka kuma rundunar ‘Yan Sandan jihar Taraba ta samu nasarar bankado wata maboyar bata gari da suka hada da masu garkuwa da mutane da kuma yan fashi da makamin dake addabar jama’a a jihar, kamar yadda kwamishinan yan sandan jihar ya tabbatar.

Wasu Masu Fashi Da Garkuwa Da Mutane Domin Kudin Fansa Da 'Yan Sanda Suka Kame.

Jihar Taraba dai na cikin jihohin dake fama da matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, batun da kwamishinan yan sandan ke cewa suna samun nasara a yanzu.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Mutum Da Ya Kashe Karamin Yaro Don Magani - 3'10"