Tarayyar Turai Ta Samarda Makudan Kudi Na Horas da Matasan Agadez A Nijar

Matasa da bakin haure da aka taso keyarsu daga Algeria zuwa Nijar

A kokarin hana matasan Agadez komawa sana'ar raka bakin haure shiga kasar Libya da gwamnatin Nijar ta haramta, tarayyar turai ta tallafa do miliyoyin kudin sefa domin horas da matasan don dogaro ga kansu

Wani abun murmushi ya zowa matasan Agadez da yanzu suke zaune babu aikin yi tun lokacin da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta haramta shiga aikin taimakawa bakin haure dake fitowa daga wasu kasashen Afirka suna ketarawa ta kasar Libya zuwa turai.

Yanzu tarayyar turai ta fito da wani tsari na horas da matasan da suke aikin tsallakawa da bakin haure. Tarayyar turan tayi tanadin saka kudi miliyan talatin na sefa domin ba matasan horo da nufin samun dogaro ga kai.

Gwamnan Jihar Agadez Salu Saloke shi yayi bayani akan wannan shirin. Matasan za'a samar masu da ayyukan yi cikin kasarsu ba sai sun fita kasashen waje ba. Kudin na tarayyar turai ya tanadi gudanar da ayyuka daban daban da zasu anfani matasa da mata

An dankawa wasu kungiyoyi alhakin gudanar da ayyukan da tarayar turai zata biya tare da hukumar dake neman kawo zaman lafiya. Shirin na tsawon shekaru biyar ne.

Hukumomin Nijar sun dukufa wajen zakulo matasan dake aikin tsallakawa da bakin haure domin su sanar dasu akan wannan sabuwar hanyar samun madogara da tarayyar turai ta kawo.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tarayyar Turai Ta Samarda Makudan Kudi Na Horas da Matasan Agadez A Nijar - 3' 21"