Taron Hukumar Kwastan ta Duniya a Abuja

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde

Ana taron kwana biyar na hukumar kwastan ta duniya a Abuja.

Hukumar kwastan ta duniya wadda ta kunshi hukumomin kwastan na kasa da kasa tana babban taronta na kwanaki biyar a Abuja babban birnin Najeriya.

Taron zai duba sha'anin matsalolin tsaro da ya addabi Najeriya da sauran makwaftan kasashe. Hukumomin suna duba hanyoyin da za'a hada karfi da karfe na tabbatar da an hada gwiwa wurin yakar matsalar tsaro da kuma sh'anin tattalin arziki da dogara ga kai tsakanin kasashen Afika.

Shugaban hukumar kwastan din Najeriya Abdullahi Dikko Inde mai masaukin baki ya yi karin haske akan taron. Yace hukumomin kwastan na kasashen dake makwaftaka da Najeriya na iya hada kawunansu domin warware matsalar tsaro da kuma hana shigowar kayan da gwamnatocinsu suka hana. Sun gane cewa duk abun da ya afkawa wata kasa ko yana da kyau ko babu zai shafi makwafciyarta.

Idan hukumomin kwastan suka hada kai suka jagoranci harkokinsu tare suna fata sojoji da 'yansanda ma zasu yi hakan saboda inganta tsaro. Idan hakan ya faru kasashe zasu zauna lafiya.

Ga rahoton Umar Faruk Musa.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Hukumar Kwastan ta Duniya a Abuja - 3' 29"