Taron Koli Kan Dakile Yahudar Cutar HIV A Afrika

shugabannin kasashen nahiyar Afrika

Taron shugbannin nahiyar Afrika ya bukaci kowacce kasa a Afrika ta kashe kashi goma sha biyar cikin dari na kasafin kudinta domin dakile nau’in wadannan cututukan

A taron shugabannin kasashen nahiyar Afrika da aka gudanar a birnin tarayya Abuja ya maida hankali kan dakile yaduwar cutar HIV, tarin fuka da zazzabin cizon sauro a kasashen nahiyar kafin shekara ta dubu biyu da talatin.

Taron ya yi bitar shekaru goma sha biyu da suka gabata da cututukan suka fi yaduwa. Taron ya bukaci kowacce kasa a Afrika ta kashe kashi goma sha biyar cikin dari na kasafin kudinta domin dakile nau’in wadannan cututukan.

Docto Abubakar Labaran Yusuf kwamishinan lafiya na jihar Kano ya yabawa ci gaba da kokarin da gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika suka yi, ya kuma ce gwamnatocin jihar Kano tana nata kokarin dabam da shirin hukumar lafiya na duniya domin shawo kan zazzabin cizon sauro.

Kwararru a fannin lafiya sun yi amana cewa, fiye da mutane dari da takwas suke mutuwa a ko da yaushe sakamakon wadannan cututuka musamman masu dauke da juna biyu.

Bisa ga cewar kwararru, cutar da tafi yiwa mata illa ita ce zazzabin cizon sauro.

Baraka Bashir ta aiko da rahoton.

Taron Koli Kan Dikele Yaduwar Cutar HIV - 1:30

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Koli Kan Dikele Yaduwar Cutar HIV - 1:43