Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Sun Gano Sabuwar Hanyar Gano Masu Dauke Da Cutar TB


Wani mai fama da cutar TB yana kwance
Wani mai fama da cutar TB yana kwance

Masana masu bincike sun gano wata sabuwar hanya ta gano mutane masu dauke da tarin fuka, ko TB, ta hanyar gano wasu nau’oin Protein dake bin jiki idan huhun mutum ya fara lalacewa.

Masana masu bincike sun gano wata sabuwar hanya ta gano mutane masu dauke da tarin fuka, ko TB, ta hanyar gano wasu nau’oin Protein dake bin jiki idan huhun mutum ya fara lalacewa.

Kwayar cutar dake haddasa tarin fuka ko TB, tana kai farmaki ne a kan huhun bil Adama, kuma irin illar da suke yi ga huhun ita ke yada wannan cutar ga wasu ko kuma ta kashe wanda ya kamu da ita. Mutane miliyan daya da rabi suke mutuwa kowace shekara a sanadin cutar ta tarin fuka.

Masana karkashin jagorancin Paul Elkington daga jami’ar Southhampton a Britaniya sun gano cewa, akwai wasu nau’oin Protein guda biyu, Collagen da Elastin, wadanda yawansu ke karuwa sosai a cikin tarin fuka.

Elkingtron yace wadannan nau’oin Protein guda biyun da ake iya gani sosai idan mutum yana dauke da cutar, zasu taimaka wajen samo sabbin hanyoyin gwaji da jinyar masu fama da ita. Ya kara da cewa, wannan zai iya bayarda damar yin gwaji kan illahirin jama’a domin gano masu dauke da kwayar cutar da wadanda suke iya yada ta sosai domin a karya lagon yaduwar wannan cuta, a tsinke hanyar yaduwarta musamman a kasahe masu tasowa inda ake fama sosai da tarin fuka.

A yanzu haka wannan kungiya tasa ta masu bincike, suna nazarin dukkan fannonin halitta da cutar tarin fuka take sanyawa su fita daga jikin huhun mutum su bi ta jinni ko wasu sassan jikinsa a yayin da cutar take kara yin karfi, bisa fatar bullo da sabbin hanyoyin gwaje-gwajen da za a iya gudanr da su a gefen gadon maras lafiya cikin sauki.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG