Taron MDD: Mai Yiwuwa Rikicin Amurka, Iran Ya Mamaye Batun Dumamar Yanayi

Zauren Majalisar Dinkin Duniya

Yayin da shugabannin kasashen duniya ke shirin hallara a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi shekara-shekara, ana ci gaba da ta-da jijiyar wuya tsakanin Amurka da Iran, batun da mai yiwuwa ya mamaye taron wanda ya kamata ya mayar da hankali kan batun dumamar yanayi.

A ranar Larabar da ta gabata, babban Sakataren Majalisar, Antonio Guterres, ya jaddadawa manema labarai muhimmancin tunkarar matsalar ta dumamar yanayi.

“Za mu dauki matakai masu armashi wajen kaucewa amfani da makamashin kwal, a kuma dakatar da ba da tallafi wajen amfani da man fetur da dangoginsa.” Inji Guterres.

Taron kolin zai fara ne daga ranar 23 ga watan nan na Satumba, inda ake sa ran sama da shugabannin kasashen duniya da wakilan gwamnati 100 za su halarta.