Tawaye Da Makamai Ba Zasu Gina Kasa ba- Shugaban Yemel.

Wani wuri da aka kai hari a Yemel

Fada tsakanin ‘yan aware da sojojin gwamnati a kudancin Yamal ya kashe akalla mutane 36, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross, yayin da shugaban kasa ke zargin mayakan da juyin mulki.

Shugaban kasa Abd Rabbu Mansour Hadi ya bukaci a tsagaita bude wuta, yana mai cewa tawaye da makamai ba zasu samar da zaman lafiya ko gina kasar ba.

Ya ce makiya na hakika sune ‘yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya, kuma komai ya faru ne a dalilin fadan.

Fadan dai ya barke ne lokacin da shugaba Hadi yayi biris da bukatar ‘yan awaren, na ya kori fara minista Ahmed Obaid Bin Dagher, da suka zarga da cin hanci da rashawa.

‘Yan awaren na samun goyon bayan daular kasashen larabawa. Wadanda ke son maido da kudancin Yamal a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Mayakan sun kame gine-ginen gwamnati masu yawa a birnin Aden, wanda ke zama babban birnin gwamnatin Hadi da kaashen duniya suka amine da ita.

Kudancin Yamal na zaman kasa mai cin gashin kanta kafin ta hade da Arewacin Yamal a alif 990.