Tennis: Frances Tiafoe, Ba'amurke Dan Asalin Kasar Saliyo Ya Fitar Da Rafael Nadal A Gasar US Open

Frances Tiafoe yana murnar doke Rafael Nadal a zagayen na hudu a gasar U.S. Open Satumba. 5, 2022, a New York.

Tiafoe shi ne na 26 a iya buga kwallon Tennis a duniya, yayin da Nadal shi ne na uku. Iyayen Tiafoe ‘yan asalin kasar Saliyo ne da suka yi kaura zuwa Amurka.

Frances Tiafoe ya fitar da Rafael Nadal a gasar Tennis ta US Open inda ya doke shi da ci 6-4, 4-6, 6-3 a zagaye na hudu.

Sau 22 Nadal dan asalin kasar Sifaniya ya lashe manyan gasar Tennis ta duniya a matakai daban-daban.

Tiafoe, mai shekaru 24, dan asalin jihar Maryland ne, ya kai zagaye na quarterfinal a karo na biyu a tarihin wasanninsa.

Wannan nasara ta Tiafoe da ta zamo abin mamaki ga masoya kwallon Tennis a duniya, na zuwa ne kwana guda, bayan da Nick Kyrgios ya doke Daniil Medevedev, wanda shi ne dan wasan Tennis na daya a duniya daga gasar wacce shi ke rike kofin.

Rafael Nadal na ficewa daga fili bayan da Tiafoe ya doke shi a ranar 5 ga watan Satumba, 2022, a New York.

Idanun Tiafoe sun rufe da hawaye farin ciki a lokacin da wasan ya zo karshe, wani abu da shi kansa ya kalla a matsayin almara – a ce ya doke Nadal

“Ji na yi kamar duniya ta tsaya cak, ban jin komai na tsawon minti daya.” In ji Tiafoe

Tiafoe shi ne na 26 a iya buga kwallon Tennis a duniya, yayin da Nadal shi ne na uku. Iyayen Tiafoe ‘yan asalin kasar Saliyo ne da suka yi kaura zuwa Amurka.