Trump: Ban Yi Watsi Da Shawarar Mataimakina Ba

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya karyata cewa da ake ya yi watsi da matsayin Mataimakinsa, Mike Pence, da sauran jami’an gwamnati, ya yi gaban kansa wajen gayyatar kungiyar Taliban a mashakatar Camp David don tattaunawar zaman lafiya.

“Da ma da shawarata na yi amfani,” abin da Trump ya gaya ma manema labarai kenan jiya Litini. Ya kara da cewa, “mun shirya ganawa. Da ma wannan ra’ayina ne, kuma soke ganawar shi ma ra’ayina ne. Ban tattauna da kowa ba.”

A wani sakon Twitter, Mista Pence ya tabbatar da abin da Trump ya fada.

“Hakika, ya Shugaban kasa. Wannan irin labaran karyar nan ne! Makiran kafafen yada labaran nan ba su ma tuntubi ofishinmu kafin su yada wannan labarin ba; da a ce sun tuntube mu, da mun gaya masu cewa da ma mu na masu cikakken goyon bayan shawarar da ka yanke.”