Trump Ya Bayyana Obama a Matsayin “Shugaban da ya Kasa”

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana tsohon shugaba Barack Obama a zaman “shugaban da ya kasa”, biyo bayan sukan lamirin matakin gwamnatin Amurka akan annobar coronavirus da Obama din yayi.

A wani jawabin kai tsaye ta hanyar internet, Obama ya shaidawa wasu daliban da suka kammala kwaleji cewa “Wannan annobar ta bayyanar da cewar wasu da ke rike da madafan iko sun gaza.” Amma bai ambaci suna ba.

A jiya Lahadi kuwa an tambayi Trump akan kalaman na Obama, sai ya ce “duba, ai shi shugaban kasa ne da ya kasa, abin da kawai zan ce kenan. “Bashi da hazaka ko kadan.”

Amurka ta zama matattarar annobar ta coronavirus a fadin duniya, inda aka sami mutum fiye da miliyan daya, da dubu 500 da suka kamu da cutar, kana mutum fiye da 90,000 suka mutu.

Masu suka sun zargi gwamnati da halin ko-in-kula da ta nuna ta hanyar yin rikon sakainar kashi ga annobar a makonnin farko na somuwarta.

Da safiyar jiya Lahadi kuma wani babban jami’an kiwon lafiyar Amurka, ya musanta cewar gwamnati ta gaza taimakawa al’ummarta.