Trump Ya Yi Kira Ga Kasashen Waje Da Su Binciki Biden

Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili yana kira ga gwamnatocin kasashen waje da su binciki abokan hamayyarsa na siyasa.

Wannan kira ya yi nuni da cewa, ya kara jaddada matakin da ya dauka a baya, wanda ya sa aka kaddamar da binciken da mai yiwuwa ya sa a tsige shi.

Da yake amsa tambayoyi a safiyar jiya Alhamis daga manema labarai a farfajiyar kudancin Fadar White House, an tambayi Trump wacce irin alfarma ya nema daga Shugaban Ukraine Volodmyr Zelenskiy, yayin kiran wayar tarho na ranar 25 ga watan Yuli, wanda hakan ya haifar da korafin mai wani kwarmata bayanan sirri.

"Ina kira da su kaddamar da bincike kan iyalan Biden." In ji Trump.

A 'yan kwanakin nan, Trump ya sha sukar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, Joe Biden, wanda yanzu haka yake sahu gaba-gaba a jerin masu neman tikitin takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar Democrat, yana mai cewa Biden ya yi amfani da karfin ikonsa ta hanyar matsawa Ukraine ta daina yin binciken wasu laifuka da suka shafi dansa, wato Hunter, wanda ya yi aiki a kamfanin makamashi na Burisma, da ke birnin Kyiv.

Trump ya zargi Hunter Biden da yin amfani da balaguron da ya yi a shekarar 2013 a jirgin shugaban kasa na Biyu – wato Airforce Two, don karbar dala biliyan 1.5 daga China a wani asusu mai zaman kansa da ya kafa.

'Yan jam'iyyar Democrat sun ce kalaman Trump din na jiya Alhamis, wani misali ne da ke nuna cewa shugaban na amfani da kujerarsa don cimma bukatunsa na kansa.