Trump Ya Zargi Puerto Rico Da Yawan Almundahana Duk Da Bala'in Guguwa

Shugaba Donald Trump

A jiya Laraba Shugaba, Donald Trump, ya kira yankin kasar Amurka na Puerto Rico “daya daga cikin wuraren da aka fi almundahana a doran kasa,” a daidai lokacin da mahaukaciyar guguwar nan ta Dorian ke dosar wannan tsibirin kasa da ke Caribbean, wanda shekaru biyu kenan da mahaukaciyar guguwar Maria ta yi kaca-kaca da wurin.

“Tsarin siyasarsu ya tabarbare, kuma ‘yan siyasarsu, au ba wadanda su ka cancanta ba ne, au mahandama ne,” a cewar Trump ta kafar Twitter. Ya kara da cewa “A baya Majalisar Dokokin Amurka ta amince da samar masu biliyoyin daloli, fiye da yadda wani wuri ya taba samu, wanda aka tura ma baragurbin ‘yan siyasar. Abin ba kyau!”

“Kuma, ba ma haka ba, babu wani abin alheri da ya taba samun Puerto Rico kamar ni!” a cewar Trump daga karshe.