Tsohon Ma’aikacin VOA Umar Sa’id Tudun Wada Ya Rasu

Marigayi Umar Sa'id Tudun Wada

Fitaccen dan jarida Alhaji Umar Sa’id Tudun Wada ya rasu bayan wani hadarin mota da ya yi akan hanyar karamar hukumar Kura da ke jihar Kano.

Hadarin ya faru ne a ranar Lahadi.

Ya zuwa lokacin rasuwar shi, shi ne shugaban gidan rediyon jihar Kano.

A wata sanarwa da aka fitar daga fadar gwamnatin Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna jimami game da mutuwar fitaccen dan jarida Tudun Wada.

Marigayi Tudun Wada ya taba aiki da gidan rediyon Muryar Amurka na VOA a Washington, inda daga baya ya rike mukamai daban-daban bayan barin shi VOA.

Ya taba rike mukamin mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, baya ga wasu mukamai da ya rike a kungiyar ‘yan jarida ta jihar Kano.

Tuni dai labarin rasuwar fitaccen dan jaridar ta karade shafukan sada zumunta, inda jama’a suka yi ta bayyana alhininsu bisa wannan rashi.