Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Zai Gurfana Gaban Kotu Bisa Zargin Cin Hanci

Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma

Ranar 6 ga watan gobe tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma zai bayyana gaban kotu akan laifuka 16 da suka hada da cin hanci

A Afirka ta Kudu, kotu ta yi sammacin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, ya bayyana gaban kuliya ranar 6 ga watan Afrilu dangane da zargin cin hanci da rashawa.

'Yan sandan kasar suka ce jiya Litinin aka baiwa tsohon shugaban kasar sammacin, mutuminda aka tilastawa yin murabus cikin watan jiya, bayan da jam'iyyar ANC ta juya masa baya.

Hukumar da take gabatar da kararraki gaban kotu ta kasar ta fada a farkon wannan wata cewa, zata nemi gurfanar da Mr. Zuma gaban kotu kan tuhume-tuhume daban daban har 16 da suka hada da cin hanci, tafiyar da harkokin kasuwanci ta hanyoyin dasuka sabawa doka, da kuma halata kudaden haram