Turkiyar Ta Kaddamar Da Harin Ramuwar Gayya Kan Siriya

Barin wuta a birnin Homs na Siriya

Jiya litinin kasar Turkiya ta kaddamar da harin ramuwar gaiya, bayan da wani hari bam daga Syria ya fada wani yankin kasar. Wannan al’amari ya auku ne, a yayinda baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon yayi kashedi dangane da mumunar sakamakon dake tattare da kamari rikicin kan iyaka.

Haka kuma Mr Ban, yace ya damu ainun da yadda ake yiwa gwamnatin Syria da yan tawaye jigilar makamai, da kuma irin tasirin da rikicin Syria zai haifar a Lebanon makwapciyar Syrian. Ya kara jadadda magance wannan rikici a siyasance da yace itace kawai mataki da za’a dauka na magance wannan rikici.

Kwana shidda a jere ke nan da Turkiya ke kai hare haren maida martini. Jiya litinin, shugaban Turkiya Abdullahi Gul yace al’amurra suna kara lalacewa a Syria, a saboda haka yayi kira ga kasashen duniya da su dauki wani mataki na magance wannan matsala.

To amma, wakilin Muryar Amirka Scott Bob ya aiko da rahoto daga kan iyakar Syria da Turkiya cewa, galibi mutane basu son Turkiya ta dauki matakin soja, domin maida martini.