VOA60 AFIRKA: An Rantsar Da Cyril Ramaphosa A Matsayin Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu, A Wani Sabon Wa’adin Shekara Biyar

Your browser doesn’t support HTML5

An rantsar da Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban kasa, a wani sabon wa’adin shekara biyar, inda ya sha alwashin yakar cin hanci, bayan da farin jinin jam’iyyarsa ta ANC ya yi dishewar da ba a taba gani ba a lokacin zabe, tun bayan da aka kawo karshen mulkin wariya a shekarar 1994.