Wani Bankin Al'umma Yayi Sama da Fadi da Kudaden Jama'a a Neja

Wasu kananan 'yan kasuwa sun fada cikin mawuyacin hali game da ajiyarsu dake wani bankin al'umma a jihar Neja.

Kananan bankuna an kafasu ne domin bada rance ga kananan 'yan kasuwa a saukake. A jihar Neja kananan 'yan kasuwa sun fi yin anfani da kananan bankuna.

To saidai yanzu kimanin watanni shida ke nan da wasu 'yan kasuwan basu iya samun kudadensu ba daga wani karamin bankin. Sunan bankin shi ne Tattali Microfinance Bank dake Makera a karamar hukumar Mashegu. Yanzu dai ma'aikatan bankin sun daina zuwa sabili da haka 'yan kasuwan basu ganin kowa a bankin.

'Yan kasuwan da suke da ajiya a bankin sun ce al'amarin ya rikitar dasu ainun. Wani Muhammad Danlami daga garin Sahorami yace sun ajiye kudadensu a bankin to amma cire kudin ya gagara. Shi kansa yana da dubu dari biyar da tamanin a bankin. Ya nemi shugaban bankin kuma ko an kirashi baya daukan wayarsa. Sunan shugaban bankin shi ne Haruna Dangajere.

Wakilin Muryar Amurka ya kira shi Haruna Dangajere ta wayar salula amma sai ya fada masa yana halartar wani taro kuma yayi alkawarin neman wakilinmu da zarar ya gama taron. Amma bai kira ba.

Kokarin jin ta bakin gwamnatin jihar Neja akan lamarin ya cutura.

Barrister Adamu Umar shugaban kungiyar lauyoyin jihar Neja ya bayyana yadda mutanen zasu bi su samu kudinsu a hukumance. Yace dunda yake babban bankin Najeriya ke kula da kananan bankuna ana iya a bi ta bankin su bayyana sunayen wadanda suka kafa bankin kana a bisu su biya kudaden mutane.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Bankin Al'umma Yayi Sama da Fadi da Kudaden Jama'a a Neja - 2' 58"