Wani Matashi Da Ake Zargi Da Dasa Bam Ya Shiga Komar 'Yan Sanda

Wasu 'yan sandan Najeriya

Wannan Lamari ya auku ne a yayin da mabiya addinin Kirista suke addu'a a cocin Living faith dake unguwar sabon tasha a Kaduna, suka lura cewa wani matashi ya bar jakarsa na tsawon lokaci a wani sashin cocin, abin da ya tilasta musu jan hankalin hukumomi.


Masu Ibada a majami’ar Living Faith dake sabon tasha a jihar Kadunan Najeriya, sun tsinci kansu cikin rudani, yayin da aka kama wani matashi mai suna Nathaniel Samuel dauke da wani abu mai kama da abun fashewa a jakarsa.

Lamarin da wasu mabiya addini kirista suke zargin sunansa Muhammad Sani ne kuma shi ba kirista bane.

Sai dai kuma shi wanda aka Kaman ya tabbatarwa muryar Amurka cewa sunansa Nathaniel Samuel ne kamar yadda rahotanni suka bayyana kuma shi ma’aikaciyan cocin ne, amma bashi da masaniya game da abin da aka gani a cikin jakarsa, kasancewar wata yarinya ce ta bashi tare da abinci.

A tattaunawarsa da wakilin Muryar Amurka Isah Lawal Ikara, shugaban kungiyar kiristoci na Najeriya a Kaduna, Rev. Joseph John Hayeph, ya ce su dai abun da suka sani shine, an kama mugun iri, addininsa ko kabilarsa bai dame su ba.

Ya kuma kara da cewa, dole ‘yan Najeriya su kau da banbancin addini da kabilanci don cin karfin bata gari wanda yace bashi da kammani na addini ko kabila.

A saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kama Wani Matashi Da Wani Abun Fashewa A Wani Coci A Kaduna