Wani Yaro Mai Shekaru 13 Ya Rasa Hannuwansa A Gombe

GOMBE: Wani malamin tsangaya ya nakasa yaro dan shekaru 13

Zubairu, almajirin makarantar tsangaya, mai shekaru 13 ya rasa hannuwansa saboda dauresu da malaminsa ya yi har suka rube akan zargin ya saci wayar salulan makwafcinsu

Malamin tsangayar da Zubairu yake karatu a wurinsa ya zargeshi da satar wayar salula a gidan makwafcinsa ne a lokacin da ya shiga domin neman kalaci.

DSP Mary Obe kakakin hukumar 'yan sandan jihar Gombe ta yiwa Muryar Amurka karin haske. Ta ce an zargi yaron da daukan wayar makwafcinsu saboda haka malaminsa ya daure hannayen yaron da igiya har hannuwan suka mutu. Maimakon a kaishi asibiti cikin gaggawa sai malamin ya dinga boye yaron. Yayinda aka kaishi asibiti hannuwan sun rube dole aka yanke. 'Yan sanda na binciken maganar.

'Yan sanda sun ce zasu kai malamin kotu ya fuskanci shari'a.

Shugaban hadakar kungiyoyin kare hakkin bil Adama na jihar Gombe ya shaida irin halin da suka sami yaron lokacin da suka ziyarci yaron a asibiti. Muhammad Aliyu ya ce yaron mai suna Zubairu almajiri ne mai shekaru 13. Da hannuwan yaron suka rube maimakon a kaishi asibiti sai aka boyeshi ana yi masa maganin gargajiya. Da suka samu labari ne suka ceto yaron suka kaishi asibiti

Kungiyoyin zasu tabbatar an yiwa yaron magani ta yadda zai samu hannu kana shi malamin an hukumtashi domin ya zama daratsi ga sauran malaman.

Gwamnan Gome Ibrahim Hassan Dankwambo ya ziyarci yaron a asibiti inda ya yi alkawarin daukan dawainiyar biyan kudin jinyarsa.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wani Yaro Ya Rasa Hannuwansa Biyu A Gombe - 3' 20"