Wasu Ma’aikata Na Bikin Ranar Dimokaradiyya Cikin Yanayin Rashin Albashi

Gwamna Darius Dickson Ishaku Na Jihar Taraba.

Yau Litinin ne ake bikin murnar ranar dimokaradiyya a Najeriya, yayin da wasu ma’aikata a jihohin Adamawa da Taraba za su gudanar da bikin ne cikin yanayin rashin albashi.

Baya ga batun rashin albashi, wasu na ganin gwamnoni basu taka rawar gani ba a cikin shekaru biyun da suka kwashe kan mulki, kamar yadda Muhammad Abacha, ‘dan jam’iyar PDP a Taraba ya tabbatar. Ya kuma gwamnati ta biya albashin ma’aikatan makaranta da na kananan hukumomi.

To amma kuma ga manazarta irinsu Mr Bako Benjamin, na ganin akwai rawar da aka taka musamman gwamnatin tarayya, ko da yake akwai abin dubawa a wasu jihohin, musamman kamar jihar Taraba inda babu wani aiki da gwamnati za ta ce tayi wa al’umma a ‘kasa.

Sau tari dai gwamnoni kan danganta rashin kudade ne da cewa suke taka musu birki, kamar yadda gwamnan jihar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya shaidawa manema labarai a Yola.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Ma’aikata Na Bikin Ranar Dimokaradiyya Cikin Yanayin Rashin Albashi - 4'14"