Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Garin Abalak  Dake Cikin Jihar Tahoua A Kasar Nijer

Labarin wasu 'yan bindiga sunkai hari a garin abalak  dake cikin jihar Tahoua a kasar Nijer a daren juma  a kan gidan mai garin abalak malam Hamed Bilu Moh’d Muktar.

Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ko su wanene ba sun kai hari gidan magajin garin Abalak Malam Hamed Bilu Mohammed Muktar,dake cikin jihar Tahoua a kasar Nijar a daren jiya.

Maharan sun kashe sojoji biyu, sun kuma yi garkuwa da wani Ba'amurke mai suna James, shugaban wata kungiyar agaji mai zaman kanta da ake kira JEMED.

A cikin hirarsu da abokin aikinmu Abdoulaziz Adili Toro ta wayar tarho, magajin garin ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ya ce ba zai iya karin haske a kai ba kasancewa a daidai lokacin suna ganawa da jami’an tsaro game da harin.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan Bindiga Sunkai Hari a Garin Abalak  Dake Cikin Jihar Tahoua a Kasar Nijer


Magajin garin yace, Muna cikin ayyuka da dama yanzu, abin gaskiya ta taba ni kwarai domin mutum ne wanda muke, tare da shi. saboda haka, ku bar yanzu, mutane biyu suka mutu, shi yasa nake so ku barni sai daga baya.

A cikin hirarsu da Grace Alheri Abdu, jim kadan bayan harin, Prof Boube Namaiwa na jami’ar Diof dake Dakar, Senegal yayi tsokaci dangane da hare haren da ake ci gaba da kaiwa jamhuriyar Nijar.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu 'Yan Bindiga Sunkai Hari a Garin Abalak  Dake Cikin Jihar Tahoua a Kasar Nijer