Wasu Yara Hudu Sun Yiwa Wata Mai Shekaru 14 Fyade

Wani mummunan laifi da ya faru a wata makaranta dake wajen Washington ya kara rura wutar zargin da ake na bakin haure marasa izinin zama na da hadari,

Bincike daga wasu kungiyoyi. ya nuna shaidar cewa bakin haure masu izini da marasa izini na aikata laifuka kasa da sauran al’umma Yan kasar, Amurka.

Iyaye , da masu zanga zanga da masu raji sun bazama zuwa makarantar Rockville High School dake Montgomery County, dake Jihar Maryland, inda ake zargin wasu yara hudu sunyi wa yarinya ‘yar ajinsu mai shekaru 14 fyade, daya daga cikin yaran bakon haure ne mara izinin zama.

Al’amarin yaja hankalin White House a farkon satin da ya gabata, inda Mai Magana da yawun white house din Sean Spicer yace fyade na daga cikin dalilan da Shugaban Kasa Donald Trump ya dage akan kame duk wasu bakin haure marasa izinin zama.

Bayani daga gwamnatin Trump ya kara jaddada barazanar manyan laifuka da bakin haure marasa izini ke aikatawa.

Amma duk da haka kungiyar Sentencing Project ta bada rahoto a wata Makala da ta rubuta inda tace “yawan laifukan da bakin haure suke aikatawa masu izinin zama da marasa izinin zaman 'kasa yake da na yan kasa wadanda aka Haifa.”