Wata Fashewa Ta Yi Raga-Raga Da Ofishin 'Yan Sandan Maiduguri

Jami'an 'yan sanda na duba wata motar da aka yi amfani da ita aka kai harin kunar bakin wake

Ana kyautata zaton cewa boma-bomai ne su ka fashe a ofishin 'yan sandan

Wata babbar fashewar da ake kyautata cewa bom ne, ta afkawa ofishin ‘yan sanda a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bada rahoton cewa Fashewar tayi raga-raga da kofar shiga harabar ofishin ‘yan sandan.

Shaidun gani da ido suka ce an rasa rayuka, mafi yawansu kuma ‘yan sanda ne.

An aza laifin kai harin a kan ‘yan kungiyar Boko haram, kungiyar da ta maida Borno tamkar sansaninta a Nigeria.