Wata Hukumar MDD Tana Bukatar Ganin Mata Sun Taka Rawar Gani a Jamhuriya ta Gaba

Majalisar Dinkin Duniya

Anyi taron bitar nasarori da ake cimma na samun kashi talatin cikin dari na mukamai ga mata da hukumar bunkasa al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNDP ta shirya a Abuja.

Matan dake rike da mukamai dama wadanda suka taba rikewa a gwamnatin Najeriya, sun duba lamarin da nuna rashin gamsuwa.

Indai dan zaben shekara ta 2015 aka shirya wannan taron, to an makara, inji Komishiniyar mata ta Gombe Hajiya Sa’adatu Mustapha, inda tace “abu yazo bakin ga’ba an koyi abubuwa dayawa, fannin da mata zasu cigaba a sha’anin siyasa, ada bazama abaki dama ki fito ba, domin an riga an shirya cewa wane shine aguri guda wane shine da guri guda to me zaka fito kayi.”

Ita kuma shugabar kungiyar raya siyasar mata dake karkashin ma’aikatar mata ta tarayya Dr. Elisa Danladi, na ganin yawan ‘da’ar matan Afirka ke sanya abarsu abaya.

Saidai wakilin hadaddiyar kungiyar nakasassu Danlami Basharu, yace indai za’a bawa mata masu lafiya kashi talatin na mukamai to mai zai hana ne abaiwa nakasassu kashi biyar cikin dari.

To kamai dai me za’a ce mata na shiga ko ana sanyasu afkawa dukkan lamura kyawawa da munana, in an duba yadda ake samun matan na jidar boma bomai su kai harin kunar bakin wake.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasarorin da Mata ke Samu - 2'58"