Wata Babbar Kotu dake zama a Abuja ta bada umarnin tasa keyar Sufeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya, Alkali Usman Baba zuwa gidan yari na tsawon watanni uku, saboda zarginsa da bijire wa umarnin kotu. To saidai Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta ce an yi bahaguwar fahimta ma yadda al'amarin yake. Ba IGP Alkali ne ya kar zomon ba.
Mai Shari’a Mobolaji Olajuwon ne ya bada wannan umarnin, biyo bayan sauraron karar da wani tsohon dan sanda mai suna Patrick Okoli ya shigar na cewa an sanya shi yayi ritayar dole daga aikin 'yan sanda ba tare da bin ka’ida ba.
Kamar yadda wakilin Muryar Amurka, Bala Alhassan ya kalato,
bayanan kotun dai sun nuna yadda aka tursasa Mr. Okoli yayi ritayar dole a watan Yunin shekarar 1992 wanda wata kotu a Bauchi a watan Fabrairun 1994 ta yanke hukunci dawo da shi bakin aiki, tare da bashi dukkan hakkokinsa.
Hukumar kula da 'yan sanda ta Najeriya dai ta bada umarnin dawowa tare da Karin girma ga Mr. Okoli a shekarar 2004 amma har zuwa shekarar 2009 da ya kara Kai kara kotu don a tursasa sufeto Janar ya maida shi aiki, abin ya ci tura.
Ofishin sufeto Janar din yayi kokarin daukaka kara amma kotu ta kori karar a shekarar 2011.
Yayin bayyana hukuncin, Mai Shari’a Olajuwon ya bada umarnin a tsare sufeto Janar na 'yan sandan a gidan yari na watanni uku ko kuma lokacin daya bi umarnin kotu.
Alkalin ya nuna bacin ransa kan yadda a matsayin sufeta Janar din na mai sanya a bi doka shi ne ke taka dokar.
To sai dai a martaninta, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce bata sane da umurnin maido da dan sandan da aka kora bakin aiki; kuma Fufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya ba zai taba yin watsi da umurnin kotu da kuma tsarin doka da oda ba.
Ta ce, “Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya na so ta bayyana karara cewa ofishin Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, bai yi watsi da umurnin kotu ko tsarin doka ba, saboda ofishinsa ma bai da wata masaniya game da wani umurnin kotu, tun lokacin da Sufeto na yanzu ya kama aiki, game wani batu wanda ke ta yawo a kafafen yada labarai na cewa IGP ya yi watsi da wani Umurnin Kotu na cewa a maida dan sandan da aka kora bakin aiki.”
Rundunar ‘yan sandan ta ce tun a 1992 aka kori dan sandan, wato ‘yan shekaru kadan bayan da IGP na yanzu ya shiga aikin dan sanda. Ta ce hatta shari’ar da aka yanke ta karshe tun a 2011 ne, wanda ke nuna cewa IGP na yanzu bai da hurumi a kai a lokacin. Saboda haka wannan labarin da ake ta yadawa na da daure kai.
Rundunar ta ce duk da haka dai IGP ya umurci Kwamishinan ‘Yan Sanda Mai Kula Da Sashin Shari’a da ya gudanar da bincike kan wannan zargin don tantanci muhallin wannan umurni na kotu sannan ya bada shawarar da ke bisa tsarin doka game da yadda ya kamata IGP ya dau mataki ba tare da bata lokaci ba.
A watan nan da muke ciki ne dai, na Nuwamba, wata alkalin kotun Abuja, Mai Shari’a Chizoba Oji, ta bada umaranin Kai shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, zuwa gidan yari na Kuje saboda bijire wa umarnin kotu. Daga baya kotun ta janye bayan sauraron karar ta EFCC.