Wata Kungiya Mai Alaka Da Al-Kai'da Ta Kashe Sojojn Chadi 10 a Mali

  • Ibrahim Garba
Wata kungiya mai alaka da al-Kaida ta yi ikirarin cewa, ita ta kai hari jiya Lahadi, kan wani sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da ke arewacin Mali

Wata kungiya mai alaka da al-Kaida ta yi ikirarin cewa, ita ta kai hari jiya Lahadi, kan wani sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da ke arewacin Mali, ta kashe sojojn Chadi 10 baya ga 25 da ta ji wa rauni.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da wanan harin, wanda ya ce ya na iya zama babban laifin yaki.

Mai magana da yawun Gueterres ya ce Sakataren na mika ta'aziyyarsa ga gwamnatin Chadi da iyalan wadanda abin ya rutsa da su. Ya kuma yaba da dukufa da juriyar sojojin tabbatar da zaman lafiya, mata da maza, wadanda su ka sadaukar da rayukansu.

Kungiyar Al-Qaida da ke yankin Maghreb na Afrika ce ta dauki alhakin wannan harin. Ta ce ta maida martini ne kan dawo da huldar diflomasiyya da Chadi ta yi da Isira'ila.