Wata Matashiya Mai Shekaru 15 Ta Doke Sarauniyar Tennis

Wata yarinya ‘yar shekaru 15 kacal da haihuwa, wacce kuma wannan ne karon farko da take shiga gasar wasan kwallon raga ta Tennis ta duniya, tayi abinda ba’a zata ba, inda ta kada tsohuwar sarauniyar wannan wasa, Venus Williams.

A karshen gwabzawar da suka yi jiya Litinin a wasan, wannan yarinyar mai suna Coco Gauff, ta samu nasara akan Venus da ci 6 da 4 da 6-4 a zagayen farko na karawar tasu.

Wannan yasa masu kallon wasan duk suka mike tsaye suna ta tafin yabawa ga wannan babban abin tarihin da karamar yarinyar tayi.

A matsayinta na ‘yar shekaru 15, Coco itace mace mafi karancin shekaru da ta taba shiga wannan wasa na Wimbledon. Venus Williams tana da shekaru 39 ne a duniya.