Wata Sabuwar Cuta Mai Shafar Numfashi Ta Bulla A Jihar Agadez

Hukumomin kiwon lafiya na jihar Agadez sun tabbatar da bullar wata cuta mai kama da Coronavirus a wani wurin hakar zinari dake karamar hukumar Tabelot. Lamarin dai ya faru ne daga ranar ashirin da shidda ga watan Fabarairu zuwa uku ga watan Maris, inda mutum goma sha tara suka kamu da cutar, wasu su biyar kuma suka rasu. A halin da ake ciki, ana jinyar wasu a babban asibitin Agadez

Cutar mai haddasa matsalar numfashi da kakin jini ta tada hankalin jama'a sosai, ganin yadda hankalin kasashen duniya ya karkata ga matsalar Coronavirus, a cewar mataimakin daraktan hukumar kiwon lafiya ta jihar Agadez Isufu Yadidi. Yadidi ya ce an tura jami'an kiwon lafiya garin Tabelot don yin bincike game da cutar, ya kuma yi kira ga mutane akan su kwantar da hankalinsu.

Wadanda suka shaida lamarin irin su Malan Gummur, sun ce hayakin wutar da masu hakar zinari ke amfani da ita ce ke janyo irin wannan illar. Yanzu dai hukumomin kiwon lafiya na Agadez na kokarin ganin sun magance wannan matsala.

Ga rahoton cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Sabuwar Cuta Mai Shafar Numfashi Ta Bulla A Jihar Agadez - 3'07"