Wayan Salula Ya Bar Aiki A kasar Sudan Ta Kudu

  • Ladan Ayawa
Yanzu haka wayan salula bata aiki a Kasar Sudan sakamakon takon sakan da akeyi tsakanin gwamnatin da kanfanin Vivacell

Daruruwan mutane ne a kasar Sudan ta Kudu yanzu haka wayan salular su bata aiki tun daga ranar jumaa.

Hakan ko ya biyo takon sakan da aka shiga ne tsakanin gwamnati da kanfanin samar da wannan wayan salula.

Wannan yasa gwamnati ta yanke layin dake aikewa da sakonni ta wayoyin hannun wato Network, a turance wanda yakai na yawan mutane kusan dubu dari 9 tun daga daren talata.

Gwamnati tace kanfanin na Vivacell yaki biyan kudin sa na lasisi.

Ministan yada labarai na kasar Michael Makuei ya fada wa muryar Amurka a farkon wannan satin cewa da farko gwamnati ce ta dauke mata biyan wannan kudin na lasisi da kuma haraji amma daga bisani kuma tace ta biya dala miliyan 66 na lasisin kuma shine kanfanin ke jankafa.

Sai dai kuma a waje daya, Pagan Amun tsohon sakataren jamiyyar Sudan Peoples Libration Movement wato SPLM, mai mullkin kasar yace kanfanin nan Vivacell ta biya kudin lasisin na shekaru da suka gabata, don haka ba hujja yanzu kuma ace kanfanin ya biya wasu kudaden lasisi na daban.

Amun yace shine wanda ya daidaita gwamnati da wannan kanfani na kasar Labanan