Waye Ya Kama Buba Galadima?

ABUJA: Buba Galadima (zaune a tsakiya) da wasu 'yan APC da ke neman ballewa

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu da ba a san ko su waye ba, sun yi awon gaba da Kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaba kasa na jam'iyyar PDP, Injiniya Buba Galadima.

Da yammacin jiya Lahadi ne labari ya yadu cewa jami'an tsaro na farin kaya wato DSS, sun je gidan Galadima suka kama shi.

Uwargidan Buba Galadima, Hajiya Fanna, ta ce a jiya Lahadi, mijinta na zaune a wajen kafin lamarin ya faru.

"Gaskiya ne (an kama shi) da yana zaune ne a gindin bishiya suna hira da wasu mutane, sai kuma suka fita masallaci inda suke salla, shi ne wata mota ta zo ta wuce wacce ba ta da lamba da mutum hudu a ciki."

Ta kara da cewa, "sai suka wuce, sai suka sake dawowa suka yi gaba suka tsaya, sai ya (Buba Galadima) ce shi bai yarda da masu motar can ba, sai kawai na ji an ce an kama shi." Inji Hajiya Fanna.

Sai dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS, ta musanta cewa ita ta kama shi.

"DSS ba ta kama Buba Galadima ba, kafafen yada labarai suna ta neman bayani daga wurinmu, amma matsayarmu ita ce ba mu muka kama Buba Galdima ba." Inji Kakakin hukumar at DSS, Peter Afonanya.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya fadawa Muryar Amurka cewa ba su da masaniya kan wanda ya kama Buba Galadima.

Shi dai Buba Galadima, ya kasance daya daga cikin mutanen da ke yawan sukar lamirinr gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Waye Ya Kama Buba Galadima? 2'37"