Wutar Rikici Na Ci Gaba Da Ruruwa A Ivory Coast

Daya Daga Cikin Mayakan Dake Goyon Bayan Outtara.

Wutar rikici na ci gaba da ruruwa a kasar Ivory Coast a daidai lokacin da mayakan dake adawa shugaba mai ci Laurent Gbagbo ke kara dannawa zuwa birnin Abdijan. Mayakan Alassane Ouattara sun sami nasarar kama birane da garuruwa kusan goma sha biyu tun bayan da suka kaddamar da wani cikakken hari a ranar litinin da ta gabata.

Shaidun gani da ido a birnin Abidjan sun ce sunji amon harbe-harbe a yau Alhamis, kuma mazauna birnin sun ce mayakan Ouattara sun balle kofar wani kurkuku sun sako illahirin wadanda ake tsare dasu.

A halin da ake ciki, hukumomin Afirka ta kudu sun bada sanarwar cewa babban hafsan rundunar sojin Ivory Coast Janar Phillippine Mangou, ya nemi da bashi mafaka a gidan jakadan Afirka ta kudu. Jiya laraba tun farko aka shirya Laurent Gbagbo zai yiwa kasa jawabi, amma anji kakakin Gwamnatinsa na cewa shugaban ya kuraido ne yaga abinda kaiya bin bayan yunkurin da ake yi yanzu.