Ya Haye Shinge Ya Dira Fadar Shugaban Amurka

  • Ibrahim Garba

Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Donald Trump ya ce matashin da ya haye shinge ya diro harabar Fadarsa na fama ne da damuwa. Jami'an tsaro kuma sun ce ba alamar wata barazana.

Wani dan kutse goye da wata jaka, wanda ya haye shingen farko na Fadar White House ya diro, an kama shi da kusan karfe 12 na daren ranar Jumma'a, a harabar Fadar ta Shugaban Amurka da ke birnin Washington DC.

Jami'an tsaron Amurka sun kama mutumin ba tare da wata tirjiya ba, kuma sun bayyana shi da Jonathan Tran, dan shekaru 26 da haihuwa, mutumin Milpitas na jahar California. Shugaba Donald Trump, wanda al'amarin bai addabe shi ba, ya ce matashin na fama ne da abin da ya kira "damuwa." Bai dai da wani tarihi na aikata laifi.

A wani rubutaccen bayani, mai magana da yawun hukumar tsaron ciki Martin Mulholland ya fadi jiya Asabar cewa babu wani abu mai hadari cikin jakkar ta Tran, kuma babu wani abin tayar da hankali da aka gano yayin da aka karade Fadar da bincike.

"Ni fa abokin Shugaban Kasa ne, mun yi da shi zan zo," abin da matashin ya gaya ma dagarawan tsaron fadar kenan. Ya kara da cewa "Haye katangar na yi."

Jami'an tsaron ciki sun dada tsaurara matakan tsaro a harabar fadar ta White House bayan da aka kutsa ciki har sau uku a watan Satumban shekara ta 2014, a yayin wa'adi na biyu na shugabancin Barack Obama.