Yadda Aka Gudanar Da Bukin Easter a Gida

Easter lokaci ne da mabiya addinin Kirista ke tunawa da mutuwa da kuma tashin Isa Almasihu kamar yadda suka yi imani, amma a wannan shekarar basu samu damar gudanar da bukin ranar ba a coci kamar yadda aka saba.

A bana, miliyoyin mabiya addinin Kirista sun gudanar da sujjada da addu'o'insu a cikin gidajensu, sabanin zuwa majami’u da ake yi, don takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Rabaran Friday Kassa da ke malami a cibiyar koyon tauhidi ta ECWA da ke birnin Jos na Najeriya, ya ce Easter lokaci ne na yin sulhu da neman gafara tsakanin mutum da mahaliccinsa da kuma sauran bil adama.

Mafi yawan majami’u sun gudanar da sujjadar Easter ta kafofin sadarwar zamani, yayin da limamai suke ci gaba da fadakar da mabiya kan muhimmancin bin dokokin da hukumomi suka gindaya don takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Saurari cikakken rahoton a sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Mutane Suka Gudanar Da Bukin Easter a Gida