Yadda Dokar Kulle Ta Kare Mutuwar Mutum Milyan Uku - Bincike

Wani bincike da aka gudanar a kwalejin Imperial London, ya nuna cewa an kaucewa mutuwar mutum milyan uku a kasashe 11 saboda dokar kulle da hukumomi suka saka tare da rufe wuraren kasuwanci da ba a fiya bukata ba da kuma makarantu.

Kasashen da aka kaucewa mace-macen sun hada da Austria, Belgium, Burtaniya Denmark, Faransa, Jamus Italiya, Spain, Sweden da kuma Switzerland.

A wani bincike na daban da aka gudanar a Amurka kuma wanda aka wallafa tare da binciken Burtaniya a ranar Litinin, ya gano cewa an kaucewa mutuwar mutum miliyan 530 daga harbuwa da COVID-19 ko an jinkirta na dokokin hana zirga zirga da aka aiwatar a China da Koriya ta Kudu da Italiya da Faransa da kuma Amurka.

Adadin wadanda suka mutu a duniya sakamakon Covid-19 ya kusa dubu 403,000 kuma wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun haura miliyan 7, a cewar bayanan da Cibiyar Nazarin Binciken Coronavirus ta Jami’ar Johns Hopkins ta tattara.