Yadda Guguwar "Dorian" Ta Isa Yankin Amurka

Wani mutum yana shanya kayansa a yankin Bahamas da guguwar ta daidaita, ranar 6 ga watan Satumba, 2019.

Mahaukaciyar guguwar da aka wa lakabi da “Dorian” ta sauka a jihar North Carolina, bayan da karfinta ya ragu zuwa mataki na daya, ta koma zallan ruwan sama da ya haifar da ambaliyar ruwa a yankunan da ke gabar tekun jihohin North da South Carolina da ke nan Amurka.

Bayan da ta sauka a jiya Juma’a, guguwar ta nausa zuwa cikin tekun Atlantika har ta kai gabashin gabar tekun Amurka, a cewar cibiyar da ke sa ido kan aukuwar guguwa.

Gabanin haka, guguwar ta daidaita yankin tsibirin Bahamas inda mutane da dama suka rasa rayukansu kana aka yi asarar dukiyoyi da dama.

“Ina matukar kaunan wannan tsibiri, matsalar ita ce, gidan da za ka gina da noman da za ka yi, da duk wasu shirye-shirye da za ka yi, duk na wucin gadi ne, saboda yadda muke yawan samun irin wannan guguwar.” Inji David Mackey, mazaunin tsibirin na Bahamas.

Guguwar ta Dorian ta yi awon gaba da daukacin unguwannin da ke Tsibirin tare da share asibitoci da filin tashin jirage.

Ya zuwa jiya Alhamis adadin mutanen da suka mutu ya kai 30, amma hukumomin yankin sun ce akwai yiwuwar adadin ya haura haka, yayin da ake ci gaba da zakulo gawarwakin mutane a baraguzan gine-gine da suka rushe.