Yadda Washington Ke Shirin Tarbar Paparoma

Paparoma Francis, shugaban darikar katolika na duniya

Amurka na shirye-shiryen taron shugaban darikar katolika na duniya Paparoma Francis, wanda ke shirin kawo ziyara a gobe Talata a Amurka.

Tun daga makon da ya gabata ne hukumomi a Amurka ke ta gargadin yadda Washingtin, babban birnin Amurka zai kasance yayin da ake shirin tarbar shugaban mabiya darikar Katolika na duniya, Paparoma Francis.

Yanzu Paparoma yana kasar Cuba inda ake asa ranz ai kammala ziyarar kwanaki uku da ya kai kasar.

Daga can ne kuma zai yada da zango a Washington sannan ya kai ziyara a birnin New York yayin da ake sa ran zai gabatar da jawabi a gaban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya.

A wannan ziyara da zai kawo Amurka, Paparoma zai gana da shugaba Barack Obama da kuma ‘yan majalisun dokokin kasar.

Ga karin bayani a wannan tattauwa tsakanin Aliyu Mustaphan Sokoto da Grace Alheri Abdu game da ziyarar ta Paparoma:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Washington Ke Shirin Tabar Paparoma 2’12”